Skip to main content

Posts

Showing posts from July, 2018

ILLOLIN SARE BISHIYOYI

SHIN KOKA   TABA YIN NAZARI   AKAN ILLOLIN   YADDA AKE SARE GANDU DAJI DAN NEMAN ITACEN GIRKI DAKUMA SAURAN BUKATU NA DAN’ADAM?   ANA SARE ITATUWA BATARE DA ANA DASA WASU BA, GA KUMA KARUWAR AL’UMMA. ANYA KUWA WATA RANA BA ZAMU NEMI BISHIYA MURASA BA KUWA? SHIN KO KATABA TUNANIN WANNAN MATSALA KAN KARUWAR AL’UMMA DA BUKATAR SU GA ITATUWA? Saran itatuwa (Deforestation) shine sare itatuwa batare da an dasa wasu ba domin bukatar dan adam. Sare itatuwa yana da illoli ga muhalli   kamar abinda ya shafi dabbobin daji da kuma karuwar shigowar Hamada (Desertification) da wasu matsaloli. A kididdigar bayanai na shekaru biyar 2000 zuwa 2005, Nigeria itace kasar da tafi kowa ce kasa fama da kwararar Hamada a duniya inda ake rasa kashi 55.7% na gandun daji. Adadin sare itatuwa a shekara a Nigeria yakai kimanin 3.5%, a tsakanin kadada (hectare) 350,000 da kadada (hectare) 400,000 a shekara. A Nigeria ana sare itatuwa ne don amfana da itatuwa, ...