Skip to main content

AMFANIN MAN HABBATTUSSAUDA DA KWAYOYINTA AJIKIN DAN ADAM



AMFANIN MAN HABBATTUSSAUDA DA KWAYOYINTA AJIKIN DAN ADAM
Yadda za ka amfani da man da irin kwaryar Habbatus- Sauda
1. CIWON SIKARI ( DAIBETES).
Ga masu fama da ciwon sikar sai su
samu zuma mai kyau su hada da man
Habbatus- Sauda a mazubi mai tsafta,
sai su gauraye wannan hadin, za su sha
cokali daya sau biyu a rana.
Sannan yana da kyau su kauracewa shan sikari da duk wani nau’in kayan abincin da
zai iya sa lallurar tayi karfi.
2. CIWON DAJI (CANCER).
Ga mai fama da ciwon daji, sai ya samu
man Habbatus-Sauda da zuma ya hada
waje guda a mazubi mai tsafta, za a
sha cokali daya kafin a ci komai da
safe, daya da rana, daya da daddare
kafin a kwanta barci
3. HAWAN JINI.
Ga mai fama da hawan jini, a kullum za
ka zuba rabin cokali na man Habbatus-
Sauda a ruwan zafi daidai yadda za a
iya sha, bayan ya huce kadan sai a sha.
Sannan a kasance masu yawan amfani
da tafarnuwa, a abinci, ko shayi , motsa jikin musamman lokacin da rana
ta fara fitowa kafin tayi zafi sosai.
4. TARI. Rabin cokali na man Habbatus -Sauda za a zuba a cikin kofi daya na shayin kofi (Coffee) za a yi haka sau biyu a rana, sannan ka shafa man Habbatus-
Sauda a kirjin ka da kuma gadon
bayanka.
5. KARIN MAHAIFA. Abinda za ki yi anan shi ne ki samu man Habbatus-Sauda da zuma za ki hada awajen guda dai-dai yawan su ya zamo daya, sai ki zuba su a mazubi daya, za ki sha rabin cokali sau uku a rana.
6. CIWON KAI MAI TSANANI Ga mai fama da matsalolin ciwon kai
sai ya samu man Habbatus-Sauda ya
shafa a gaba goshin sa, sannan ya dan
diga kadan a hanci, bayan ga haka ya
kasance mai cin irin habbatus-Sauda
bayan an gasa shi kadan tare da zuma, akalla sau biyu a kowace rana.
7. MURA DA SANYI Ga mai fama da mura sai ya samu zuma su hada da Man Habbatus-Sauda, sai ya sha rabin cokali a kullum sannan su diga man kadan a cikin hanci.
8. TSURO A KAN FATA. Abinda za ka yi , shi ne sai ka nika irin kwayar Habbatus- sauda , sai ka kwaba da ruwa, sannan ka shafa akan wannan tsoron. Sau biyu a rana.
9. MATSAlOLIN DA SUKA SHAFI HANCI DA MAKOGWARO. Ga mai fama da irin wannan matsalolin, sai ya samu lemun tsami mai kyau, ya matse ruwan a kofi
sannan ya zuba ruwan zafi sosai akai,
rabin cokali na man habbatus- Sauda,
sannan sai ya shaki wannan tiririn ruwan zafin. Haka zai yi sau biyu a rana
10. INGANTA LAFIYAR FATA Habbatus- Sauda za ki samu sai ki hada da man zaitun , sai ki wanke fuskar , wannan hadin za ki shafa a fuska , bayan awa daya sai ki wanke.
11. ZUBEWAR GASHIN KAI. Ga mata masu fama da matsalar zubewar gashi, sai su hada man Habbatus_Sauda da man Zaitun, bayan su tsefe gashin sai su bi layi-layi na gashin suna sa masa man tare da yiwa kan tausa. .
12. CIWON KUNNE. Irin kwayar Habbatus-Sauda za ka gasa shi sama-sama, sannan ka ni ka shi , sai ka sa man Habbatus- sauda rabin cokali, man Zaitun rabin cokali, sai ka hadesu a mazubi mai kyau, sirinji zaka samu sai ka dure wannan hadin maganai aciki, zaka diga akunne sau biyu a rana,
13. GURBACEWAR CIKI. Ga mai fama da, gurbacewa ciki , sai ya sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda a cikin kofi daya kindirmo daya. Za ka sha sau biya a rana.
14. INGANTA KARFIN GARKUWAR JIKI – Shan man Habbatus-Sauda na kara
inganta karfin garkuwar dan Adam
musamman in zai juri shan rabin
cokali a kowace rana.
15. CIWON BAYA. Ga amasu fama matsalolin ciwon baya sai su , samu kamar cokali 1-2 na man Habbatus- Sauda sai ya dora akan wuta yayi dan dumi, wannan man zasu shafa a bayan su tare da yiwa wajen tausa , a hankali. Sannan su sha man Habbatus- Sauda, karamin cokali sau uku a rana.
16. RAGE DAMUWA. Ga masu fama da yawan damuwa , ko kuma su ji duk sun takura , sai su sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda a shayi ko kuma a kofe ( coffee).
17. MATSALOLIN AL’ADA Ga mace mai fama da matsalolin da suka shafi al’ada sai ta samu zuma cokali daya ta zuba a kofin ruwan dumi, sannan ta sa karami cokali na man Habbatus-Sauda, sai ki sha sau biyu a rana, har na tsawon kwana 40.
18. CIWON KIRJI Ga masu fama da ciwon kirji, sai ya samu, man Habbatus-Sauda ya hada da zuma a waje daya, bayan su hada, sai su shafa a daidai inda yake ciwon tare da lailaya man sosai ta yadda zai ratsa cikin jikin sosai, sannan a sha cokali daya da safe da kuma yamma a kullum.
19. TSUTSAR CIKI Ga mai fama da tsutsar ciki, sai ya nika irin kwayar Habbatus-Sauda guda 14 , sai ya hada da rabin karamin cokali na man Habbatus-Sauda tare da rabin- rabi karamin cokali na ruwan kal ( apple cider vinegar) sai a hada da ¼ litar ruwa. In shaa Allahu za’a samu sauki.
20. SHAKUWA. A duk sanda ka ke fama da shakuwa sai ka tauna irin kwayar Man Habbatus- Sauda guda 7, kasha ½ cokali na Man Habbatus_Sauda tare da (butter) Man shanu.
21. MAGANCE MATSALOLIN MAFITSARA. Abinda za ka yi a duk sanda ka samu kanka a irin wannan yanayi sai ka, samu ¼ na litar nono/kindurmo ka
hada da ½ cokali na Man Habbatus-
Sauda da cokali daya na zuma, sai ka
hade su waje daya, zaka sha wannan akullum sau 2.
22. HASKEN FATA. Man Habbatus-Sauda na da amfani wajen haskaka fata, ba tare da ya haifar da wata illa ba. Abinda za ki yi, shi ne ki samu gram 50 na Man
Habbatus-Sauda da gram 50 na Man
Zaitun sai ki hada waje guda, za ki sha karamin cokali daya a kullum kafin cin
abincin safe.
23. KUTURTA( LEPROSY). Ga mai fama da ciwon kuturta sai su matse lemun zaki a kofi daya sannan ya sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda ya juya sosai, za ya sha sau biyu a rana. In shaa Allahu za’a samu waraka.
24. AMOSARIN GASHIN KA. Man Habbatus-Sauda 10 grams za ki
hada da 30 grams na man Zaitu sannan
ki zuba 30 grams na lalle na gargajiya
a ciki, kwabasu za kiyi sannan ki dan
dumama shi akan wuta, bayan ya dan
huce sai ki shafa wannan kwabin akan, sannan ki sa hular lede bayan minti
15-30 sai ki wanke, za ki iya yin haka
sau biyu a sati.
25. ZAFIN JIKI. Aduk sanda ka samu kanka a cikin yanayi na zafin jiki, sai ka zuba rabin cokali na man Habbatus-Sauda a cikin shayi mara madara, sai ka sha. Zaka iya cigaba dayi har sai zafin jikin yayi sanyi.
26.KURAJEN FUSKA. Ga masu fama da matsalolin kujane fuska sai ki samu abarba ki markadata sannan ki tace ruwan abarba a kofi, sai ki dauko man Habbatus-Sauda ki sa rabin cokali na man Habbatus-Sauda, in kuma baki da abarba sai kiyi amfani da lemun tsami mai manya-manya a maimakon abarba.
Za ki sha kafin kici abinci da kuma da daddare kafin ki kwanta barci har na tsawon wata 1, sannan za ki iya amfani (Kalonji pimple cream) na fuska. Yana da kyau ki daina cin abincin da zafi sosai.
Wandanna sune akdan daga cikin
amfani ko tasirin Mai da kwayar irin
Habbatus-Sauda ke samarwa ga lafiyar
jikinmu.
Amma abinda hankulan mu anan shi ne , in kazo siyan man Hbbatus-Sauda ko irin yana da kyau ka kula sosai , don wasu ana siyar masu da “ black caraway” amatsayin Man Habbatus-Sauda wanda kowanen su abu ne mabambanta. Sannan yana da kyau ka kula da iya adadin da za kayi amfani da shi , domin amfanin da shi har yar zarta, ma’ana ya wuce misali na iya illatar da kai.
Man Habbatus-Sauda, ana kiran sa da suna daban- daban, aduk inda ka ga an rubuta suna kamar haka “ Kalonji, Black
cumin, Habal-al-baraka.” To shi ne black
seed oil wato Habbatus-Sauda.
Lafiyarka jarinka.
AMFANIN HABBATUSSAUDA DON MAGANCE KOWACE IRIN MATSALA
habbatussauda tana da amfani sosai don manzon Allah(s.a.w) yace nahore ku da habbatussauda, don tana magance kowace irin cuta in banda tsufa ko mutuwa malaman duniya sun tabbatar,da cewa tana maganin kowace irin cuta
GAMSAR DA MIJI A WAJEN KWANCIYA SHINE ZAMAN AURENKI Zuma farar saka. Garin miski. Ki hadesu ki tace da abin tata, sa ki dinga dangwala da auduga kina matsewa a gabanki da daddare ko ya rage awa daya kafin saduwa. Wanna yana jawowa mace dadi.
LALACI WAJEN KWANCIYA
lalaci a wajen kwaciya da miji ba karamar illa bace a cikin rayuwar auratayya,
ko mace taji bata Sha'awa.
ko mace taji ta a bushe kamas.
ko ta dinga jin Zafi in an sadu da ita.
ko kuma mace Daga namiji ya taba ta taji kamar ta mutu.
ko kuma ayi amfani da mace tace bata ji komai ba.
ko gabanta ya matse.
Wata har yankewa takeyi.
Duk kuma wannan na faruwa ne ta sanadiyar rashin kula da Kai da rashin sha abinda yake Akwai.
IRIN WANNAN SAKACIN DA MATA SUKE YI SHI YAKE JAWO IRIN WADANNAN MATSALOLIN.
amma ba Zan bar Ku haka ba Zan taimaka muku da wasu Daga cikin magunguna irin wadannan matsalolin.
Rashin ni'imar mace yana jefa ta a cikin irin wanna.
ga kuma sanyi a jikinta.
wata kuma basur ya cinye ta ya danne Mata ni'imar.
BASUR DA SANYI SUNA DA ILLA A GURIN MACE
BAYANI AKAN CIWON BASIR(dan kanoma)
Kamar dai Yadda kuka sani Wannan Ciwon Yana Addabar Maza da Mata, In shaa Allahu zamuyi bayanin wannan Ciwon.
MAGANIN BASIR
Idan basir yayi tsiro Ana samu danya, zait lauz, a kwaba shi da danyan kwal egg a dinga
turawa a cikin dubura, yana kashe basir mai tsiro ,kuma yana konar da basir da yake toshe bakin dubura.
CIWON BASIR
a samu ganyen riyhan busasshe sai a daka shi yayi laushi sannan a samu man zaitun ko habbatussauda sai a kwaba a rinka cusawa ta dubura.
Za a yi haka sau biyar a yini daya.
2
A samu shibtu a rinka hadawa da Zuma ana sha a kuma rage kadan a rinka cusawa a dubura.
a dinga shan habbatussauda safe da yamma
Ko zuma
man zaitun
Suna magani basir
3.
A samu za'afaran a daka shi a hada shi da kwaduwar kwai egg danye a rinka sha safe da yamma.
🥒 🍃 4
A samu wadannan mahadan
fulful
citta
tafarnuwa
gishiri
Sai a daka su waje daya a rinka dibar cokali daya ana hadawa da Zuma Ana sha sau daya safe da yamma.
da yawa mutane suna kasa banbancewa meye basir,da yawa mutum daga yaji cikinsa yana kugi ko yana ciwo sai yace basir yana damunsa, amma da yawa wasu cututtu suna kama da basir kuma yana cutarwa da yawa, yakan sa sha'awar mutum ta bangaren jima'I ta dauke, ya kansa ciwon ulcer domin yana hana cin abinci, yana kuma kawo wata cuta wadda ake ce wa (sha'awatul-kaziba), shine
mutum daya fara cin abinci sai yaji ya koshi.
MAIDA TSOHUWA YARINYA
duk matar da take son gabanta ya matse kofar ta zama karama kamar na budurwa, sai a samu ya'yan bagaruwa da ganyenta a tafasasu a rinka zama cikin ruwan ta yanda zafin ba zai cutarba, anaso kullun ayi hakan sau daya insha Allah zai matse ya zama karami,kuma koda akwai wasu kuraje masu fitowa sunayin kai-kai duk zasu mutu da ikon Allah : wani hadin kuma: shi wannan hadi za a tanadi kayayyaki kamar
haka:
🍉- kankana mai zaki
🍍 abarba mai kyau
🍠 gwanda mai kyau
🍎 apple(mai ja sosai)
🥛 madarar ruwa(luna ko peak)
🍯 zuma
wadannan kaya zaki hadasu guri daya sai ki
markadasu, kitacesu,sai ki saka suga ko
mazankwaila ki rinka sha wannan hadin yana da kyau sosai musammam ga amare ko masu niyyar yin aure wani hadin kuma: zaki samu ya'yan hulba sai ki sami karanfani
da kuma ya'uan habbatulbaraka da kuma zuma dukkansu cokali bibbiyu 2 zuma kuma cokali hudu 4 sai ki dafasu su dahu sai ki sauke inya huce sai ki rinka sha kina kuma kama ruwa dashi yanada kyau sosai.
DON KARIN SOYAYYA TSAKANIN MATA DA MIJI DA KUMA MOTSA SHA'AWA:
- zaki samu nikakkiyar alkama cokali biyar 5
- ki samu garin dabino cokali goma 10
- ki samu garin farar shinkafa cokali biyar 5
- ki samu garin sha'ir cokali biyar 5
- ki samu nonon akuya
idan kika hadasu guri daya sai ki samu zuma mai
kyau sosai sai ki barshi yayi kwana uku 3 sai ki
daukoshi ki dafashi inya dahu sai ki dinga sha, ki
jaraba ki gani yanada kyau sosai,musamman
larabawa suna amfani dashi sosai
GA WANI HADIN DON MATSEWAR GABAN MACE
wannan hadin ana yinshi shima don karin ni-ma da kuma matsawar gaban mace,kuma yana sa hankalin mai gida yadawo kanki,sannan kuma yana sa gaban mace kamshi sosai wannan hadin angwada amfani yana aiki sosai kayan da ake bukata sune:
- lemun tsami
- zuma mai kyau
- raihan
yanda ake yi shine: zaki yayyanka wannan lemun tsamin sai ki sakashi a ruwan dumi sai ki kawo raihan ki zuba, sai ki kawo zuma ki zuba sai ki rinka kama ruwa dashi tare da wanke duk wani lungu da sako na gabanki ciki da waje,yin hakan yana sa mai gida ya rinka tabo maki majiya dadi wannan wani bangare ne a cikin gaban mace.
YANDA GABAN MACE YAKE:
mafi yawa daga cikin mutane basu san
yanda gaban mace yake ba balle su san cewa akwai wani waje da ake kira majiya dadi, kuma sanin hakan yana da muhimmanci domin duk macen da tayi sa'a mijinta yana tabo mata wannan wuri(majiya dadi) to zata ga son da yake mata yana karuwa dari bisa dari(100%) itama haka zata ji tana kara sonshi sosai
MATSALAR CIWON SANYI GA MACE
1 Ana samun tafarnuwa abare ta sai a dauki daya Ayi matsi da ita a gaba.
Idan an wayi gari asamu garin HULBA a tafasata sai mace ta zauna cikin ruwan idan ya dan huce.
Ayi haka har kimanin kwana 7 amma shi na
tafarnuwa za'a yi ko sau 2 ko 3 ya isa 2 Dangane da magance ciwon sanyi asamu
hulba
Bagaruwa
man habbatussauda
Yadda za'a yi abine a hada bagaruwa da hulba a tafasasu sai idan ya dan huce sai azauna ciki sannan kuma ashafa man habbatussauda kamar yadda za'ayi matsi insha Allah yazo daya daga cikin wadannan magunguna da
akayi amfani dashi zai magance matsalar ciwon sanyi sannan kowane yana Kara dawwamar da ni'ima ga mace in kuma akwai zai karasa wasu nau'in na magance matsala rashin sha'awa da kuma karawa mace ni'ima shine asamu.
*NONON RAKUMI*
*GARIN RIDI*
a hadasu guri daya a rinka sha 6
Asamu lemun tsami a yankasu sai a saka shi
cikin ruwan zafi idan ya jika sossai sai a fiddo lemun yakkakken da aka saka cikin ruwan zafin a dinga wanko kowane lungu da sako na farjin mace sannan ruwan sai a Kama ruwa dasu.
*MATSALA KAWOWA DA WURI GA MAZA*
watau daya fara saduwa da mace ba zai dauki dogon lokaci ba yana harka sai ya kawo ba tare da ita macen ta gamsu ba, uwargida sai ki nemi
cucumba gurji
zuma
zaki markada cucumbar ba tare da kin fere ba saiki ki zuba zuma a ciki zaki iya sakawa a cikin firji, domin sanyi saboda
maigida yaji dadin sha:
GYARAN GASHI
Muddin uwargida na kokarin gyaran gashi lokaci lokaci, za ta kiyaye gashin nata daga karairayewa, zai rika laushi kuma ya kara tsawo. Domin cimma wannan, za ki tanadi ganyen magarya, ki rika wanke
da shi, yana kara karfafa gashi ya kuma hana shi zubewa. Ga wadansu daga cikin sinadaran da za ki tanada:
1. Man zogale.
2. Man kwakwa.
3. Man zaitun.
Sai ki hade su guri guda ki rika shafawa a kanki a matsayin man kitson ki, ko kuma ki tanadi:
1. Danyen kwai sabulun salo
2. Sabulun salo
3. Garin shammar
A fasa kwai, amma banda kwaiduwar farin kadai za
ki yi amfani da shi, sai ki zuba sabulun salo a ciki, ki
matse ki zuba garin shammar ciki sai ki wanke kai
da shi. Allah ya taimake mu.
Ga wani hadin kuma dai duk na gyaran gashi wannan
hadin na masu karamin karfi ne domin abubuwan da
za ki tanada ba za su fi karfin ki ba da farko za ki
tanadi ruwan Tumatur ne da sabulun salo kawai za ki
matse ruwan tumatir din sai ki zuba sabulun salon a
ciki ki barshin ya samu tsayin minti talatin idan ya
jika, sai ki shafa a kanki da dadare.
Idan zaki kwanta bacci, da safe sai ki sanya ruwan
dumi ki wanke tas. Insha Allah za ki ga gashinki ya
yi kyau sosai.
Wannan kuma man gashi ne mai sa laushin gashi da
tsawo ya yi baki yana shekin haske. Wannan hadin ba
zai taba barin gashin ki ya kare raye ba kuma zai rika
laushi sosai. Da farko zaki tanadi:
1. Zaitun shitta
2. Man alayyadi
3. Man zaitun
4. Man kwakwa
5. Man albasa
6. Man hulba
7. Man ridi
Za ku hada hulba da lalle gudaya sai ku tafasa, sai
ku tace ku wanke kai da shi, sannan ku hade dukan
wannan mayuka da na lissafo ku rinka shafawa a
kan ku zaku ga gashin ku yana kara kyau.
✎・ Gyaran Tafin Kafa・✎
‘Yan’uwana mata yanzu zan yi bayyani ne a kan
yanda za mu kula da tafin kafanmu, ba ku b a zuwa
wajen wanke kafa, kawai za ku yi amfani da wannan
hadin kuma za ku ga abin mamaki. Ga ababen da za
ku tanada:
1. Man shanu
2. Man kwakwa
3. Man ridi
4. Man alayyadi
Zaku hade wanan mayukan gu daya, idan kafa tana
tsagewa ko tana kaushi, da daddare idan za ki
kwanta bacci sai ku shafa wannan mayukan a tafin
kafarku sai ku sami leda ku daure kafar da shi ku
kuma saka safa (socks) da safe ku wanke kafar da
ruwan dumi ku shafa man zaitun da man ridi. Ko
kuma ku nemi:
1. Man kwakwa
2. Man shanu
3. Man zaitun
Sai ku hade su gudaya suma kuringa shafawa da
dare kuma saka leda kuna daure kafar sannan kusa
sake safa (socks) idan gari ya waye ki fara gasa
kafar kadan sannan ki wanke da ruwan dumi, ki
shafa masa man zaitun.
Wannan hadin wanke kafa ne sai a tanadi:
1. Kokumba
2. Halle
3. Man ridi
Sai ku tanadi ‘Cucumber’ ku fere bayan ku yanyanka
shi kanana, a markada, amma fa kar a cika masa
ruwa domin an fi son ainihin ruwan ‘Cucumber’ din
sai a kwaba lallen da ruwan cucumber din, a rika
amfani da shi da dare, ana cirewa a wanke da safe,
ku kuma wanke kafar da ruwan dumi sai a shafawa
kafar man ridi insha Allah, indai aka rike wannan
hade-haden, za a ga amfaninsa, kuma za a yi
mamakin irin kyan da tafin kafar ku zai yi. Allah ya
taimakemu.
Rage kiba da tumbi
Mata da dama ba su son kiba da tumbi, wannan
kuma ba komai yake jawo shi ba sai haihuwa da
wadansu matsalolin. Galibi, maza ba su cika son
masu kiba ko tumbi ba. Amma akwai hanyoyin
gyarawa. ‘Yan’uwa, za a iya gwada wannan hadin
domin biyan bukata:
1. Garin hulba
2. Ganyen na’a-na’a
3. Garin kanamfari
4. Zuma
5. Lemon tsami
6. Farin kwalli
7. Man na’a-na’a
Za a hade wadannan ganyen guri guda, a sa mi farin
kwalli dunkullale, za a saka a ciki, idan ya kai kamar
minti biyar sai a cire sannan a saka zuma a cikin
ruwan sai ku rika sha, shi kuma man na’a-na’a, za a
rika shafawa a tumbi ne zai ragu insha Allahu.
Idan kuma ana son rage kibar ne gaba daya sai a sa lemon tsami a ruwan a rika sha. Nan ma wani hadin ne na rage kiba za ku tanadi:
1. Habbatus-sauda
2. Sukari
3. Ganyen shayi dan aune
4. Zuma
Wannan hadin zaki hade su guri guda ku tafasa su ku
zuba zuma a ciki sai ku rinka sha.
. GYARAN JIKI AMARE DA UWARGIDA
Amfanin Garin Hulba Don Gyaran Jiki
Gyaran Fuska
Za ki samu garin hulbar ki dama da madara da
zuma ya damu sosai sai ki shafa a fuskar ki, ki
barshi kamar minti talatin kafin ki yi wanka, fuskar ki
zata yi sheki zai kashe miki pinplesya gyara miki
fuska kuma yana maida tsohuwa yarinya.
Gyaran Gashi
Wato shi gashi wani abu ne wanda ke matukar
karawa mace kyau da kima shi yasa yake da kyau
mu dinga gyara gashin kanmu akai akai wato kuma
aduk abun gyara gashi ba kamar hulba, ga masu son
gashin su ya yi tsawo da sheki zaki hada garin hulba
coconut oil ki gauraya sosai sai ki shafa akanki ki
barshi yadadi akalla kamar, awa daya ko ma fiye da
hakan, kuma zaki ringa yin hakan kama sau biyu a
sati guda, sannan zaki kiyi na mako uku, yana kara
tsawon gashi, kuma gashin kanki zaiyi kyau da sheki,
kuma yana hana karyewar gashi.
Ga masu amosani, wato dandruff, zaki hada hulba
da apple cider ko ruwan khalki shafa a kanki, da san
dare ki barshi har gari ya waye, gabaki daya amosari
zasu mutu kuma gashin ki zai yi kyau.
Gyaran Cikowar Kirji ( NONO )
Babu kamar hulba yana gyara sosai kuma yasa
kirjinki ya cicciko ya kara girma da kyau, wasu suna
zuba garin hulba ciki abinci kullum sunaci don
gyaran kirji in har abun ya zame masu jiki yana gyara
sosai, kuma bayan cikar kirji ma yana warkar da
cuttutuka da dama a jiki.
Haka kuma iya samun kindirmo mai kyau sai ku
hada da hulba kuma shay ana aiki biyu ne farko
gyaran kirji na biyu kuma sa ni’ima.
Ga wanda kirjin su ya kwan biyu suna iya hada garin
sa da kundirmo, sannan su sami mansa suna shan
spoon daya da safe daya da rana daya da marce,
bayan haka ma suna iya dafa garinsa su tace su sa
tsuma su gasa kirjin su da shi sannan kuma su hsafa
wa kirjin man sa.
Magana ta karshe anan kuma abin fahimta, ba’aso
mace mai juna biyu ta sha hulba domin yana kawo
nakuda da gagawa. Na biyu mata masu shayarwa
suna iya hada garin hulban a cikin abincin su yana
kara nagartaccen ruwan mama, kuma zai sa jinjiri ya
kasance cikin koshin lafiya.
Karin Bayani Game Da Karin Ni’imar Mace
Kamar yadda muka sha yin bayani a baya dangane
da karin ni’ima a jikin mace, har kullum muna dada
fadada wannan bangaren, inda a kullum masana
harkar kiwon lafiya ke gudanar da karin haske kan
wannan batu.
Uwargida za ki iya samun sassaken Baure, ki dafa
shi sai bayan ya dafu sai ki juye ruwan sai ki samu
mazarkwaila da zuma da kanunfari da citta, ki zuba
aciki, ki tafasa ki rika sha safe da yamma.
Masana tun tabbatar da cewa dukkanin macen da ke
amfani da wannan, za ta samu karin ni’ima a jikinta,
sannan ta kasance mai dimbin alheri ga maigidanta.
Bayan haka, za ki iya samun totuwar rake mai
tsafta, sai ki bar shi ya bushe, ki samu Bagaruwa
guda uku da Almuski da Kanumfari, ki hada su, waje
daya ki rika tsuguno kuma ki rika goga zaitun a jiki,
musamman a gabanki, hakan zai kara miki ni’ima
mai yawae.
Bayan wannan, za ki iya samun RIDI, ki wanke shi,
ki nika har sai ya zama gari, ki bar shi, ya bushe, ki
rika sha da nono, zai kara miki ni’ima gasken-gaske,
musamman wajen ibadar aure. Haka kuma yana
maganin dattin mahaifa. Dangane da masu neman
karin girman mama da sauransu…? A kullum na kan
yi kokarin bayyana musu wasu irin sinadaran da za
su yi amfani da shi, amma kuma suna bukatar karin
bayani. Abin sani shi ne wasu matan daga sun yi
haihuwa daya, za ka ga nononsu ya zube, wannan
yana saka maigida, musamman irin mazan da suke
son ganin mace da cikar mama cikin damuwa, wasu
ma sai ya haifar musu da neman sabon aure.
Don haka uwargida, ki samu Habbatus-Sauda, Hulba,
Alkama, Gyada, Ridi, Danyar shinkafa da Busassen
Karas, duk ki daka su waje daya, kina sha da
madarar ruwa na gwangwani, misali PEAK. Kina iya sha sa’o’i biyu akalla kafin barci da kuma Sa’o’i biyu bayan kin farka daga barcin.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

AMFANIN KANUMFARI A JIKIN DAN ADAM

 AMFANIN KANUMFARI   A JIKIN DAN ADAM Sunan Kanumfari ya samo asali ne daga Larabci wato Qaranful, don da Turanci sukan ce masa Cloves ne, ana noma shi galibi a tsuburai ne, mu dai nan Afurka akan same shi ne a tsuburin Pemba da Zanzibar na qasar Tanzaniya, kusan Kanumfarin da wadannan tsiburan suke fitarwa ya ishi nahiyar tamu gaba daya, a qasar Indonesia aka san shi, ko ma a ce qasarsa kenan ta asali, akan yi aiki da shi don abicin da ake sa wa sukari kamar fura, kunu, buredi, nakiya da sauransu, akan kuma sa a duk abincin gishiri don qara qanshin abincin. Kanumfari ya qunshi abubuwa da dama game da lafiyar jikin dan adam, kamar Vitamin A, C, K, Iron, Calcium, Potassium, Magnesium, Phosphor, Sodium, Manganese, yana da Calories 21, Fats 1.32, Saturated fats 0.35, Carbohydrates 4.04, Fibres 2.3, Proteins 0.39, Cholesterol 0, kenan Kanumfari fari zai iya zama babban abin da mutum zai buqata don rayuwarsa ba ma wai don qanshin abinci ko abin sha ba. 1)...

MAGANIN KARFIN MAZA(MEN POWER) DA NAMIJIN GORO.

MAGANIN KARFIN MAZA(MEN POWER) DA NAMIJIN GORO.  A yau zamuyi bayanin hanyar da za'a bi domin samun karfin mazakuta cikin sauki ba tare da kashe kudi ba,kuma wannan hanya bata da illa ga lafiya,sai dai kara lafiya.  ZA'A SAMU 1. Garin Namijin goro 2. Zuma Da farko za'a samu Zuma tacecciya mai kyau a kwaba ta da garin Namijin goro sai a rika shan chokali 3 sau 2 a rana,zakai mamaki sosai.