AMFANIN KANUMFARI A JIKIN DAN ADAM Sunan Kanumfari ya samo asali ne daga Larabci wato Qaranful, don da Turanci sukan ce masa Cloves ne, ana noma shi galibi a tsuburai ne, mu dai nan Afurka akan same shi ne a tsuburin Pemba da Zanzibar na qasar Tanzaniya, kusan Kanumfarin da wadannan tsiburan suke fitarwa ya ishi nahiyar tamu gaba daya, a qasar Indonesia aka san shi, ko ma a ce qasarsa kenan ta asali, akan yi aiki da shi don abicin da ake sa wa sukari kamar fura, kunu, buredi, nakiya da sauransu, akan kuma sa a duk abincin gishiri don qara qanshin abincin. Kanumfari ya qunshi abubuwa da dama game da lafiyar jikin dan adam, kamar Vitamin A, C, K, Iron, Calcium, Potassium, Magnesium, Phosphor, Sodium, Manganese, yana da Calories 21, Fats 1.32, Saturated fats 0.35, Carbohydrates 4.04, Fibres 2.3, Proteins 0.39, Cholesterol 0, kenan Kanumfari fari zai iya zama babban abin da mutum zai buqata don rayuwarsa ba ma wai don qanshin abinci ko abin sha ba. 1)...
Comments
Post a Comment