Skip to main content

Posts

An Kera Na'urar Robot Da Zata Iya Zuwa Cefane

An Kera Na'urar Robot Da Zata Iya Zuwa Cefane WASHINGTON DC, —  Wani kamfanin da ya shahara wajen kirkirar na'ura mai sarrafa kanta (Robot) don taimakawa jama’a gudanar da ayyukan yau da kullun, ya fadada aikin da na'urar da suke kirkira zata dinga yi. Kamfanin Starship tare da hadin gwiwar kamfanin Co-op Milton, sun kammala kirkirar wanta na'ura da zata zama 'yar aike, wadda za ta iyimwa mutane cefane, ko sayo abinci a gidajen sayar da abinci. Masana na ganin wannan tsarin zai dauki lokaci mai tsawo kamun wadannan na'urorin su zama jiki, mutane su saba da su da amincewa da irin ayyukan su. Robot din na tafiya cikin saurin da ya kai nisan kilomita 16.1 cikin awa daya, kuma zai iya shiga cikin taron jama’a don isar da sako batare da ya bace ba. Kamfanin zai wadatar da wannan na'urar a cikin birnin Landon daga nan zuwa shekarar 2019. Robot din kuma na dauke da kyamara guda hudu da na'urar GPS don gane idan akwai wata matsala a hanya don canzawa idan bukata...
Recent posts

Za A Kayata Shafin Facebook Da Bangaren Masu Neman Aure

Za A Kayata Shafin Facebook Da Bangaren Masu Neman Aure WASHINGTON DC, —  Shahararren kamfanin sadarwar yanar gizo Facebook, ya bayyana kudirin sa na kayatar da shafin sa da bangaren ‘Manema Aure’ shugaban kamfanin Mr. Mark Zuckerbeg, ne ya bayyana haka, kamfanin zai fadada hanyoyin kyautatama jama’a. Mark, ya sanar da hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da injiniyoyi masu kirkirar manhajoji, a wani taron kara wa juna sani mai take F8, ya kara da cewar, damar zata kara hada mutane a fadin duniya, da niyyar samar da karuwar auratayya ta hanyar amfani da yanar gizo. Domin kuwa akwai kimanin mutane milliyan dari biyu da suka bayyanar kansu a matsayin samari da ‘yan mata marasa aure a shafin su na facebook, wanda hakan ya nuna cewar akwai bukatar kamfanin yayi wani abu don ba mutane damar haduwa da masoya. Kamfanin dai ya shahara wajen sadar da zumunci a yanar gizo, tun dai a shekarar 2004 yake ba jama'a dama a shafin su bayyana ko suna da aure ko kuma A'a.. Ya kuma kara da cewar, k...

Sabuwar Manhajar Masoya Ta Facebook Za Ta Tona Mazambata

Sabuwar Manhajar Masoya Ta Facebook Za Ta Tona Mazambata WASHINGTON D.C —  Sabuwar manhajar nan ta masoya da kamfanin Facebook ya bada sanarwar fitowa da ita kwanan nan, zata taimaka wa masu amfani da shafin wajan ganowa da fallasa masu amfani da shafin wajan yaudarar mutane ta hanyar amfani da hotunan da ba nasu ba da kuma bayanan karya domin cimma wani buri nasu na daban, da kuma masu satar bayanan jama’a a yanar gido. Kamfanin wanda ya fuskanci kalubale da dama akan rashin kare bayanan masu amfani da shafin sa lamarin da ya sa har majalisar dokokin Amurka ta gayyaci shugaban kamfani Mark Zuckerberg, domin amsa tambayoyin a majalisa. Manhajar zata ba jama’a masu shekarun da suka kama da 18, damar bude shafi a manhajar wadda zata basu damar bayyana ra’ayin su akan irin mata ko mazan da suke so su nema ba tare da dukkan abokan da ke bin su sun gani ba. Daga karshe wannan manhaja zata nuna inda mai shafin yake da kuma irin abokan da yake mu’amula da su da kuma kara dankon zumunci ts...

Kimiyya Da Fasaha Kan Iya Zama Hadari Ko Alheri Ga Rayuwar Yau Da Kullum

Ana iya kiran wannan ci gaba irin na mai hakar rijiya kuwa? Ganin yadda karuwar fasahar zamani ke kara zama wani abu, da duniya take kara dunkulewa waje guda, domin a yanzu har kasashe masu tasowa a duniya suna samun ci gaban zamani. Lura da yadda ake samun bunkasa a fannin kimiyya da fasaha a wannan zamani, wasu na dasa alamar tambaya - shin ana iya kiran wannan ci gaban a matsayin abu mai alfanu ga duniya kuwa, lura da yadda yake barazana ga fannonin rayuwar dan adam ta yau da kullum? Masana na ganin hakan yana iya zama tattare da wasu abubuwa da sai an nutsu kafin a samu amsoshinsu. Idan muka yi dubi kan fannin bunkasar fannin sadarwa, ana iya amfani da damar wajen aikata barna a doron kasa, ba kawai sai ta satar bayanai ba, ana iya amfani da kafofin wajen ganin an shiga cikin kundin bayanai na kasa wajen sanin sirrinta da duk wasu tsare-tsare da suke da su a bangaren tsaro ga kasarsu. A cewar shugaban wata cibbiyar bincike Tom Siebel, ci gaban kimiyya da aka samu a duniya na tattar...

AMFANIN TAFASA GA DAN ADAM.

AMFANIN TAFASA GA DAN ADAM. Tafasa wadda muka sani a kasar Hausa wata karamar bishiya ce da ke da ganye launin kore da fure da kananan ‘ya’ya a jikinta. Ita dai wannan bishiyar ana samun ta a wurare da dama a kasashen Afirka ciki har da Nijeriya musamman a jihohin Arewa. A kasar Indiya masu maganin Ayurbedic Herbal Medicines sun dauki lokaci mai tsawo suna amfani da tafasa dan yin maganin wasu kebabbun rashin lafiyoyi kamar haka: Maganin makanta ko matsalar da ta shafi ta gani. A baya ga wannan matsala ta barazanar na makanta, tafasa na kara lafiyar ido kama daga yara har zuwa tsofaffi. Domin haka sai a tunga yin miyan tafasa ana ci a abinci. Wani bincike da wasu masana tsirran itatuwa suka yi sun tabbatar da cewa Tafasa na maganin wasu cututtukan da ke shafuwar babbar hanzanya da kuma taurin bahaya. -Tafasa tana maganin zafin ciki da kuma wanke dattin ciki da ya cushe. -Tafasa tana rage kiba dan haka wannan wata damace ga masu tumbi wadanda ke bukatar rage nauyi, sai a nemi ganyen taf...

DOMIN RAGE TUMBI /TEƁA/ƘIBA.

DOMIN RAGE TUMBI /TEƁA/ƘIBA.   Game da masu sun rage tubi ko kiba to ga hanya mai sauki cikin kankanin lokaci zaka ga sakamako mai kyau.  ZA'A NEMI. 1. Danyar citta 2. Lemon tsami 3. Zuma. YADDA ZA'A HADA.  Da farko zaka feraye cittar ya zamana fatar dage saman nata ka cire ta,sannan ka yayyanka ta kanana,ka samu ruwa kofi 1 ka  dura a kan wuta sannan ka zuba cittar,bayan nan sai ka kawo lemon tsami kamar guda daya ka matse shi ka saka har bawon a cikin ruwan.    Bayan tafasa sai ka sauke ka bar shi ya wuce sannan kasa zuma a ciki daidai gwargwado kasha,zakai haka sau biyu a rana na tsawon wani lokaci zaka ga canji sosai.  Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama salati.

MAGANIN KARFIN MAZA(MEN POWER) DA NAMIJIN GORO.

MAGANIN KARFIN MAZA(MEN POWER) DA NAMIJIN GORO.  A yau zamuyi bayanin hanyar da za'a bi domin samun karfin mazakuta cikin sauki ba tare da kashe kudi ba,kuma wannan hanya bata da illa ga lafiya,sai dai kara lafiya.  ZA'A SAMU 1. Garin Namijin goro 2. Zuma Da farko za'a samu Zuma tacecciya mai kyau a kwaba ta da garin Namijin goro sai a rika shan chokali 3 sau 2 a rana,zakai mamaki sosai.