Skip to main content

Sabuwar Manhajar Masoya Ta Facebook Za Ta Tona Mazambata

Sabuwar Manhajar Masoya Ta Facebook Za Ta Tona Mazambata

Sabuwar manhajar nan ta masoya da kamfanin Facebook ya bada sanarwar fitowa da ita kwanan nan, zata taimaka wa masu amfani da shafin wajan ganowa da fallasa masu amfani da shafin wajan yaudarar mutane ta hanyar amfani da hotunan da ba nasu ba da kuma bayanan karya domin cimma wani buri nasu na daban, da kuma masu satar bayanan jama’a a yanar gido.

Kamfanin wanda ya fuskanci kalubale da dama akan rashin kare bayanan masu amfani da shafin sa lamarin da ya sa har majalisar dokokin Amurka ta gayyaci shugaban kamfani Mark Zuckerberg, domin amsa tambayoyin a majalisa.

Manhajar zata ba jama’a masu shekarun da suka kama da 18, damar bude shafi a manhajar wadda zata basu damar bayyana ra’ayin su akan irin mata ko mazan da suke so su nema ba tare da dukkan abokan da ke bin su sun gani ba.

Daga karshe wannan manhaja zata nuna inda mai shafin yake da kuma irin abokan da yake mu’amula da su da kuma kara dankon zumunci tsakanin jama’a a cewar jami’an kamfanin. Mun samo wannan labara ne daga mujallar Washington post, ta kasar Amurka.

Comments

Popular posts from this blog

AMFANIN MAN HABBATTUSSAUDA DA KWAYOYINTA AJIKIN DAN ADAM

AMFANIN MAN HABBATTUSSAUDA DA KWAYOYINTA AJIKIN DAN ADAM Yadda za ka amfani da man da irin kwaryar Habbatus- Sauda 1. CIWON SIKARI ( DAIBETES). Ga masu fama da ciwon sikar sai su samu zuma mai kyau su hada da man Habbatus- Sauda a mazubi mai tsafta, sai su gauraye wannan hadin, za su sha cokali daya sau biyu a rana. Sannan yana da kyau su kauracewa shan sikari da duk wani nau’in kayan abincin da zai iya sa lallurar tayi karfi. 2. CIWON DAJI (CANCER). Ga mai fama da ciwon daji, sai ya samu man Habbatus-Sauda da zuma ya hada waje guda a mazubi mai tsafta, za a sha cokali daya kafin a ci komai da safe, daya da rana, daya da daddare kafin a kwanta barci 3. HAWAN JINI. Ga mai fama da hawan jini, a kullum za ka zuba rabin cokali na man Habbatus- Sauda a ruwan zafi daidai yadda za a iya sha, bayan ya huce kadan sai a sha. Sannan a kasance masu yawan amfani da tafarnuwa, a abinci, ko shayi , motsa jikin musamman lokacin da rana ta fara fitowa kafin tayi zaf...

AMFANIN KANUMFARI A JIKIN DAN ADAM

 AMFANIN KANUMFARI   A JIKIN DAN ADAM Sunan Kanumfari ya samo asali ne daga Larabci wato Qaranful, don da Turanci sukan ce masa Cloves ne, ana noma shi galibi a tsuburai ne, mu dai nan Afurka akan same shi ne a tsuburin Pemba da Zanzibar na qasar Tanzaniya, kusan Kanumfarin da wadannan tsiburan suke fitarwa ya ishi nahiyar tamu gaba daya, a qasar Indonesia aka san shi, ko ma a ce qasarsa kenan ta asali, akan yi aiki da shi don abicin da ake sa wa sukari kamar fura, kunu, buredi, nakiya da sauransu, akan kuma sa a duk abincin gishiri don qara qanshin abincin. Kanumfari ya qunshi abubuwa da dama game da lafiyar jikin dan adam, kamar Vitamin A, C, K, Iron, Calcium, Potassium, Magnesium, Phosphor, Sodium, Manganese, yana da Calories 21, Fats 1.32, Saturated fats 0.35, Carbohydrates 4.04, Fibres 2.3, Proteins 0.39, Cholesterol 0, kenan Kanumfari fari zai iya zama babban abin da mutum zai buqata don rayuwarsa ba ma wai don qanshin abinci ko abin sha ba. 1)...

MAGANIN KARFIN MAZA(MEN POWER) DA NAMIJIN GORO.

MAGANIN KARFIN MAZA(MEN POWER) DA NAMIJIN GORO.  A yau zamuyi bayanin hanyar da za'a bi domin samun karfin mazakuta cikin sauki ba tare da kashe kudi ba,kuma wannan hanya bata da illa ga lafiya,sai dai kara lafiya.  ZA'A SAMU 1. Garin Namijin goro 2. Zuma Da farko za'a samu Zuma tacecciya mai kyau a kwaba ta da garin Namijin goro sai a rika shan chokali 3 sau 2 a rana,zakai mamaki sosai.