ZOGALE DA AMFANINSA
Zogale wani nau'in itacene wanda
mutane, aljanu, dabbobi da tsirrai, hatta kasama tana anfanuwa da shi, wani
abin mamaki yadda halittun ruwa suke
amfanuwa da jijiyar sa idan tana kusa da ruwa. Kadan daga cikin amfanin zogale:
amfanuwa da jijiyar sa idan tana kusa da ruwa. Kadan daga cikin amfanin zogale:
1. A shafa danyen ganyen zogale akan
goshi, yana maganin ciwon kai.
2. Ga wanda ya yanke, sare ko karfe
yaji masa rauni, ya shafa danyen ganyen zogale awajan jinin zai tsaya .
3. Maifama da kuraje ajiki, a hada
garin zogale da man zaitun a shafa.
4. Anasa garin zogale akan wani
rauni ko gembo, zaiyi saurin warkarwa.
5. Sanya garin zogale acikin abinci
na maganin Hawan jini da karama mutum kuzari. kara karfin garkuwar jiki,
taimaka wa zagayawar jini da bugawarsa.
6. Mai ciwon ido da kunne a diga
ruwan danyen zogale.
7. A dafa furen zogale da zuma, yana
karin ruwan nono.
8. Mai cutar yawan fitsari
(Diyabetis) ya rinka yin shayin furen zogale da citta.
9. Shayin furen zogale da Albasa
yana maganin sanyi
10. A dafa ganyen zogale da zuma
asha kamar shayi, yana maganin Olsa (ulcer).
11. A dafa ganyen zogale tareda
kanwa yar kadan yana maganin shawara.
12. Hakama cin danyen zogale yana
maganin tsutsan ciki ga yara.
13. A daka ganyen zogale da 'ya'yan
'baure asha a nono ko kunu yana maganin ciwon hanta ko koda.
14. Asoya 'ya'yan zogale adaka ahada
da man kwakwa (man ja) anashafawa yana maganin sanyin kashi da kumburi.
15. Adaka zangarniyar zogale da
'ya'yan jikinta tareda kananfari, citta,masoro da kimba yana karin karfin
namiji da kuzari haka ma yana karawa mata Nishadi.
16. Saiwar zogale da 'ya'yan kankana
asha da nono yana maganin sakuwar ciki (wato Apendis).
17. Idan Aljani yabuge mutum ya
fadi, a shaka masa ganyen zogale ahanci, aljanin zaifita ko yayi magana.
18. Shanruwan dafaffan zogale yana
rage radadin cutar kanjamau (Aids),Typhoid, malaria da basir ko shawara,
ayawaita shan ruwan dan waraka.
19. Saukake narkar da abinci.
20. Wanking ciki, musam man idan aka
cishi kafin aci komai.
21. Rage kiba.
22. Gyara kwalwa .
23. Yana magance karancin abinci mai gina jiki.
24. Yawan amfani da shi na taimakawa masu cutar sikla.
22. Gyara kwalwa .
23. Yana magance karancin abinci mai gina jiki.
24. Yawan amfani da shi na taimakawa masu cutar sikla.
25. Idan akajefasa a ruwa zai tace
(filtration) ruwan.
Comments
Post a Comment