Shin KO KUNSAN cewa Taurari suma suna mutuwa?
Shin ko kasan cewa idan tauraro ya tashi mutuwa ya kan fashe ne ya tarwatse yafada cikin Black Hole?
Shin ko kasan cewa black hole wani katon (Babban) rami ne wanda yake mazaunin kabari (grave) na dukkan wani tauraro tayadda idan wani tauraro ya mutu yakan fada cikin sa?
Shin ko kasan cewa duk girman tauraro idan tauraro yafada cikin ramin black hole to kamar a jefa kwayar wake ne a cikin rijiya saboda girman ramin black hole?
Shin ko kasan cewa black hole yasami wannan suna ne saboda tsananin duhun dake cikin sa?
Shin ko kasan cewa ramin black hole yana dauke da "gravitational force" mai tsananin karfin gaske ta yadda duk wani abu idan yazo kusa da wajen to gravitational force dake cikin ramin yakan janyo abin zuwa cikin ramin?
Shin ko kasan cewa hatta haske (light) idan ya gifta ta wajen ramin black hole yakan zuke hasken?
Shin ko kasan cewa Allah (SWT) Ya halicci black hole ne daga "Neutrons" wanda ake samu a jikin kowani "atom"?
Shin ko kasan cewa Allah (SWT) Yayi magana akan black hole a cikin Al-Qur'ani a cikin surah Waaqi'ah ayar da Allah yake cewa: "Fala UQsimu bimawaa Qi'in-nujuum'' ?
Wannan shine hoton black hole , zakuga taurari gasunan 'yan kananu . sannan ga ramin black hole nan a tsakiyar wajen, duk da fa akwai tauraron da idan ya fado wannan duniyar tamu zai
iya rufeta gaba daya, amma idan ya fada ramin black hole baifi girman kwayar dawa ba.
HAKIKA ALLAH DA GIRMA YAKE SHI KADAI YAKE BASHI DA ABOKIN TARAYYA MAMALLAKIN ABINDA KE CIKIN SAMMAI BAKWAI DA KASSAI BAKWAI SUBHANAHU WATA'ALA
Comments
Post a Comment