MAGANIN SAMUN HAIHUWA,TA YARDAR ALLAH.
Ko shakka babu Allah shi yake bada haihuwa ma Wanda yaga dama a lokacin da ya ga dama, amma wannan ba ya hana mutum Neman magani masamman in ya samu jinkiri Wanda yawuce na al’ada.
Dalilai da yawa yakan janyo rashin samun haihuwa tsakanin ma’aurata, amma Wanda yafi shahara shine kamar:
– Low sperm count a wajen maza.
– Hormonal imbalance.
– Weakness of the ovaries awajen mata.
– Blockage in the fallopian tubes a wajen mata.
– Wasu nau’i na infections da sauransu.
Dukkan wadannan ana iya zuwa asibiti domin ayi gwaji a tabbatar cewa babu daya daga cikin matsalolin da muka ambata, idan kuma aka samu matsalan to lalle yazama dole a maganceta sannan daga bisani ayi amfani da wannan magani da zan ambata yanzu:
Asamu taceccen Zuma mai kyau litre biyu, sannan a samu gram sittin 60 gram na Hububulluqa a hada a garwaya sosai sai dukkan biyun mata da mijin suke shan cokali daddaya safe da yamma har tsawon wata hudu, insha Allahu za’a dace cikin watanni uku na farko.
Abin sadaqa ayiwa Annabi Salati.
Comments
Post a Comment